GWAMNAN JIHAR BAUCHI SANATA BALA MUHAMMAD YAYI TA'AZIYA WA ƳAN UWA DA IYALAI NA LIMAMIN MASALLACIN GWALLAGA MARIGAYI IMAM IBRAHIM IDRIS.
A wannan Litinin ne Gwamnan jihar Bauchi Sanata Bala Abdulƙadir Muhammad ya jagoranci tawagar Muƙarraban gwamnatinshi zuwa unguwar Jahun suka gabatar da ta'aziyar su na rasuwar limamin masallacin Izala na Gwallaga Marigayi Imam Ibrahim Idris wanda Allah yayi mishi rasuwa a wajen jinya a kasar Masar a makon da ya gabata.
Da yake gabatar da ta'aziyar a madadin kanshi iyalanshi da gwamnatin jihar Bauchi Sanata Bala Abdulƙadir Muhammad yayi Addu'ar Allah ya gafarta mishi ya sanya Aljanna ta kasance Makoma a gareshi.
Gwamnan ya bayyana babban Marigayin a matsayin babban Malami da ya dade yana karantarwa da da bada tarbiyya wa Al'umma.
Sai ya bukaci ƴaƴanshi da sauran Malamai da suyi koyi da irin kyawawan halaye tarbiyya da ya koyar tare da fatar Allah ya basu haƙuri da juriyar rashi.
Da yake jawabi a madadin ƴan uwa da iyalai Shugaban kungiyar Izalah ta jihar Bauchi Farfesa Zubairu Abubakar Madaki yayi godiya ne gwamnan da sauran Muƙaraban gwamnati da suka rufa mishi baya zuwa ta'aziya.
Sai yayaba wa gwamnan bisa wannan kyakkyawar dabi'a da ya Assasa na shi lungu da sako na jihar Bauchi domin gabatar da ta'aziyar fatar Allah ya basu ladar ta'aziya.

Comments
Post a Comment