GWAMNAN JIHAR BAUCHI SANATA BALA MUHAMMAD YAYI TA'AZIYA WA BABBAN SAKATARE NA MA'AIKATAR AYYUKA DA SUFURI ENGR. HAMISU GARBA BISA RASUWAR IYALINSA.
A wannan juma'ah ce gwamnan jihar Bauchi Sanata Bala Abdulƙadir Muhammad tare da rakiyar wasu Muƙarraban gwamnatinshi suka gabatar da ta'aziyar rasuwar Marigayiya Hajiya Husaina Abubakar matar Babban sakatare na Ma'aikatar Ayyuka Engr. Hamisu Garba a Unguwar Tudun Salmanu dake cikin garin Bauchi.
Da yake gabatar da ta'aziyar a madadin kanshi, iyalanshi gwamnatin jihar Bauchi Gwamna Bala Abdulƙadir Muhammad yayi Addu'ar Allah ya gafarta mata ya sanya Aljannah ta kasance Makoma a gare ta.
Sai ya bayyana rashin Mata a matsayin babban rashi tare da fatar Allah ya bada Mijinta da sauran iyalanta Hakuri da Juriyar rashi,
Da yake jawabi a madadin Iyalai Alh Ladan Garba Ilelah yayi godiya ne wa gwamnan da Muƙarrabanshi ladar ta'aziya.

Comments
Post a Comment