GWAMNA BALA MUHAMMAD NA JIHAR BAUCHI YA KAI ZIYARAR BAZATA SAKATARIYAR ABUBAKAR UMAR NA JIHAR










TARE DA YIN KIRA GA KWAMISHINONI, MANYAN SAKATARORI DA SAURAN MA'AIKATA KAN SU MAI DA HANKALI KAN AIKINSU.


A wani mataki na ganin an kawo gyara da dawo da martabar aikin gwamnati a jihar Bauchi, 

Gwamnan jihar Sanata Bala Abdulƙadir Muhammad ya kai ziyarar Bazata a sakatariyar Abubakar Umar na jihar domin duba yadda Ma'aikata suke zuwa aiki tare da duba aikin gyaran wani bangare na sakatariyar.


Da yake jawabi bayan ya zaga wasu Ofisoshin ma'aikatu a sakatariyar Gwamna Bala Abdulƙadir Muhammad ya nuna rashin jindadinsa bisa yadda ya tarar da wasu manya da ƙananan ma'aikatan basu bakin aiki a ofisoshinsu tare da yin kira ga kwamishinoni da Manyan sakatarorinsu da su maida hankali kan Ayyukansu tare da zuwa aiki da wuri , yana mai cewa rashi zaman wasunsu a ofisoshin yana bada gudumawa na rashi zaman ƙananan ma'aikatan a wajen aikinsu.


Yana mai cewa zai cigaba da kai irin wannan ziyarar a ma'aikatu da hukumomin gwamnati domin ganin an dawo da martabar aiki.


Da yake maida jawabi shugaban Ma'aikata na jiha Dr. Yahuza Adamu Haruna yayi godiya ne wa gwamnan bisa ziyarar tare da kira ga Ma'aikata da su mai da hankali kan aikin su, wajen zuwa aiki a kan lokaci da kuma tashi a lokacin tashi

 

Comments

Popular posts from this blog

Bauchi State Celebrates Engr. Joshua Sanga as National Chairman of Nigerian Institute of Water Engineers (NIWE)*

PDP BAUCHI SOUTH PLEDGES CONTINUES SUPPORT TO GOVERNOR BALA ABDULKADIR MOHAMMED.

WE WILL AUGMENT THE CONTRACTOR TO COMPLETE THE AZARE MODERN MARKET CONSTRUCTION PROJECT