GWAMNAN JIHAR BAUCHI SANATA BALA MUHAMMAD YAYI TA'AZIYA WA GWAMNAN JIHAR JIGAWA NA RASUWAR MAHAIFIYARSA DA ƊANSHI.

 








TARE DA ADDU'AR ALLAH YA MUSU RAHAMA


A wannan Asabar ne gwamnan jihar Bauchi Sanata Bala Abdulƙadir Muhammad ya jagoranci tawagar Muƙarraban gwamnati zuwa Garin Kafin Hausa a jihar Jigawa domin gabatar da Ta'aziyar su wa gwamnan jihar Jigawa Alh Umar A Namadi bisa rasuwar Mahaifiyarshi da Ɗanshi.


Da yake jawabi yayinda yake gabatar da ta'aziyar a madadin kanshi da gwamnatin jihar Bauchi, Gwamna Bala Abdulƙadir Muhammad yayi Addu'ar Allah ya gafarta musu, ya sanya Aljanna ta kasance Makoma a garesu,


Gwamnan ya bayyana rashin Mahaifiya da Ɗa a lokaci guda a matsayin babbar jarabawar, sai yayi fatar Allah ya bashi haƙuri da juriyar rashi.


Da yake maida jawabi gwamnan jihar Jigawa Alh Umar A Namadi yayi godiya ne wa gwamnan da Muƙarrabanshi bisa tayashi nuna Alhinin rashin da yayi, yana cewa wannan ƙaddara ce daga Ubangiji kuma kowa da lokacin shi, sai yayi fatar Allah ya basu ladar ta'aziya.

Comments

Popular posts from this blog

Bauchi State Celebrates Engr. Joshua Sanga as National Chairman of Nigerian Institute of Water Engineers (NIWE)*

PDP BAUCHI SOUTH PLEDGES CONTINUES SUPPORT TO GOVERNOR BALA ABDULKADIR MOHAMMED.

WE WILL AUGMENT THE CONTRACTOR TO COMPLETE THE AZARE MODERN MARKET CONSTRUCTION PROJECT