DUK WANDA YAZO BAUCHI KO SHINE SARKIN HASADA YAGA IRIN AYYUKAN DA GWAMNA BALA MUHAMMAD YAYI DOLE YA YABA MAKA YAYI MAKA FATAR ALHERI, A CEWAR SHEIKH SANI YAHAYA JINGIR.


 



A cigaba da ziyarar ta'aziyar rasuwar Yadukon Gwamnan jihar Bauchi Hajiya Hauwa Muhammad da ake zuwa wa gwamnan a wannan karo ya karɓi Tawagar Sheikh Sani Yahaya Jingir Shugaban Majalisar Malamai na ƙasa na kungiyar Izalah wacce Alsheikh Isma'ila Idris ya Assasa a wannan Talatar a gidan Gwamnati.


Da yake jawabi yayin ta'aziyar Sheikh Sani Yahaya Jingir ya tunatas da Al'umma ce darasin dake tattare da Mutuwa tare da yin Addu'ar Allah ya gafarta mata ya bayar wa gwamnan da sauran Iyalanta Hakuri da Juriyar rashi.


Haka nan Sheikh Sani Yahaya Jingir yayi amfani da damar wajen yaba wa Gwamna Bala Abdulƙadir Muhammad bisa irin Ayyukan da gwamnatinshi take shinfiɗawa a faɗin jihar Bauchi, yana mai cewa "ko Mutum shine Hasidin Iza Hasada ya shigo Bauchi ya san ta canza, kuma duk wanda yaga ginin gidan gwamnati Bauchi da gwamna Bala Muhammad yayi yasan bayayi wa kanshi bane domin baginin da za'a more shi ba ne na shekara goma ko ashirin ba" 


Sai shehin Malamin yayi godiya wa gwamnan bisa Ayyukan gina Masallatai da makarantu wanda a cewarsa irin Ayyukan da suka sabbaba Ƙaunar dake tsakaninsu ke nan, tare da Addu'ar Allah ya dafa wa gwamnan wajen samun nasarar Jagoranci da yake yi.


Da yake Maida jawabi gwamnan jihar Bauchi Sanata Bala Abdulƙadir Muhammad yayi godiya ne bisa irin ƙauna da shehin Malamin da Magoya bayan shi suke nuna masa, Sai yayi Addu'ar Allah ya basu ladan ta'aziya, 


Kan gwamna Bala Muhammad ya buƙaci malamin da yayi Magana wa shugaban ƙasa da ya riƙa sauraran Al'umma, saboda yana ƙoƙarin aiwatar da sabon dokar haraji wanda a cewar masana ba Alheri bane ga Ƴan Najeriya musamman ma Arewa.


Yana mai cewa gwamnoni da Al'ummar ƙasar nan sunyi mishi magana yaƙi sauraran su,


Amma yana zaton Shehin Malamin a matsayinshi na jigo wanda ya taka rawa wajen Zaɓansu in har yayi mishi magana zai saurareshi.


Sai ya jaddada goyon bayansu da godiya wa malamin game da irin tarbiyar da suke koyar da Al'umma tare da Addu'ar Allah ya ƙaramishi tsawon rai da nisan kwana a kan gudumawar da yake bayar wa Musulunci.

Comments

Popular posts from this blog

Bauchi State Celebrates Engr. Joshua Sanga as National Chairman of Nigerian Institute of Water Engineers (NIWE)*

PDP BAUCHI SOUTH PLEDGES CONTINUES SUPPORT TO GOVERNOR BALA ABDULKADIR MOHAMMED.

WE WILL AUGMENT THE CONTRACTOR TO COMPLETE THE AZARE MODERN MARKET CONSTRUCTION PROJECT