Gwamna Bala Muhammad ya Nuna Ɓacin Ran sa biyo bayan sake samun Rahoton Sace Yara daga Jihar Bauchi zuwa Jihar Anambra
Gwamnan jihar Bauchi Sanata Bala Muhammad ya karɓi Yara Uku ƴan Asalin Jihar Bauchi wanda aka sace tare da Sayar dasu a jihar Anambra.
Da yake jawabi yayin karɓan Yaran, Gwamna Bala Muhammad ya nuna Ɓacin Rai sakamakon ƙaruwar rahotannin satar yara a Jihar Bauchi inda ya ɗaura alhakin hakan ga Sakaci daga wasu iyaye da kuma Talauci.
A cewar Gwamnan, wannan lamari na baya-bayan nan ya nuna tsananin matsalar da kuma bukatar a ɗaukar matakin gaggawa, sannan ya bukaci a sauya tunani, yana mai jaddada cewa dole ne iyaye su dauki nauyin kula da rayuwar ‘ya’yansu.
Gwamna Mohammed ya jaddada mahimmancin shigar da al’umma wajen magance matsalar tare da yin kira ga masu gidaje, shugabannin gargajiya, da sauran masu ruwa da tsaki da su dauki nauyin tabbatar da tsaro da tsaron yara a yankunansu.
Kwamishinan Ƴan Sanda a Jihar Bauchi ya bayyana sunayen yaran da aka sacen wanda suka haɗa da Sabo Salisu dan shekara 3, Isah Abdulkadir mai shekaru 4, da Nana Khadija Zakariya’u mai shekaru 6.
Suleiman Musa Kwankiyel
Mataimaki Na Musamman Ga Gwamna Bala Muhammad Ɓangaren Sadarwa.
08-01-2025



Comments
Post a Comment